in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Afirka na shirin kulla yarjejeniyar fadada ciniki cikin 'yanci
2015-06-10 11:06:55 cri

Shugabannin yankunan gabashi da na kudancin nahiyar Afirka, na shirin rattaba hannu kan wata yarjejeniya, wadda za ta share fagen kaddamar da babban yankin ciniki cikin 'yanci, wanda zai hade da dama daga kasashen dake nahiyar.

Ana sa ran sanya hannu kan wannan yarjejeniya ne yau Laraba a kasar Masar, karkashin inuwar kungiyoyin raya tattalin arziki na EAC da SADC, da kuma kasuwar bai daya tsakanin yankunan gabashi da kudancin nahiyar Afirka ko COMESA a takaice.

Tuni dai mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto ya tashi zuwa Masar domin halartar taron da za a gudanar karkashin kungiyoyin uku. Ruto, wanda zai wakilci shugaban Kenya Uhuru Kenyatta a taron, ya ce, makasudinsa shi ne samar da hanya mai sauki, ta shige da ficen hajoji, da zirga-zirgar al'umma, da saukaka ayyukan ba da hidima tsakanin kasashen yankunan biyu.

Ya ce, sanya hannu kan yarjejeniyar zai kuma ba da damar karfafa hadin gwiwa, da cudanyar kasashen yankin, musamman a fannonin bunkasa tattalin arziki, da na zamantakewar al'umma, ta hanyar cinikayya cikin 'yanci a kasuwar bai daya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China