in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe 10 za su halarci bikin bajen kolin cinikin kasa da kasa a Najeriya
2014-02-07 12:00:57 cri

A kalla kasashe goma ne suka tabbatar da halartarsu a dandalin kasuwancin kasa da kasa karo na 25 na Enugu a cikin watan Maris mai zuwa a kudu maso gabashin kasar Najeriya.

Hukumar kula da harkokin kasuwanci, masana'antu, ma'adinai da noma ta Enugu (ECCIMA) ta ba da wannan labari a yayin wani taron manema labarai kan shirye wannan bajen koli na kasa da kasa a ranar Alhamis a Enugu.

Shugaban ECCIMA, Ifeanyi Okoye ya bayyana cewa, kasashen za su hada da Malaisia, Indiya, China, Vietnam da Amurka. Kuma kamfanonin Najeriya fiye da 600 za su halarci bikin baje kolin, in ji shugaban, ya kuma bayyana cewa, wasu karin kasashen Afrika sun bayyana niyyarsu ta halartar wannan dandali.

Taken baje kolin na wannan karo zai kasance "kara karfafa yin takarar kayayyakin da Najeriya take sarrafawa a kasuwannin duniya", in ji mista Okoye.

Haka kuma ECCIMA ta dauki duk wasu matakan tsaron da suka wajaba, da samar da ruwa da wutar lantarki yadda ya kamata da kuma samar da kebabbun wurare masu inganci ta yadda baki za su ji dadi.

"Wannan baje kolin zai zama wani abin tarihi, domin za mu yi iyakacin kokari domin cimma babbar nasara da samun karuwa daga wajen bangarorin mahalarta." in ji mista Okoye tare da bayyana cewa, a wannan karo, bangaren noma zai rike muhimmin matsayi, bisa burin karfafa samar da albarkatun noma da kasuwancinsu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China