in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan kungiyoyin tattalin arzikin Afirka na shirya kafa yankin ciniki maras shinge
2014-11-02 10:25:41 cri
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Ruwanda suka bayar, an ce, manyan kungiyoyin tattalin arzikin Afirka guda uku wato kungiyar EAC, da ESA da kuma SADC sun cimma daidaito kan kafa yankin yin ciniki maras shinge na yankunansu. Ana sa ran cewa, za a kaddamar da gina yankin kafin karshen shekarar nan.

A gun taron ministocin kungiyoyin uku da aka kammala a birnin Bujumbura dake kasar Burundi, an sanar da cewa, za a kaddamar da yankin yin ciniki maras shinge na kungiyoyin uku a gun taron koli na kungiyoyin da za a gudanar a watan Disamba na bana a birnin Alkahira dake kasar Masar.

Yankin din yana shafar kasashe 26 na Afirka, yawansu ya kai rabin membobin kungiyar AU, kuma yawan mutanen kasashen ya kai miliyan 625, yawan GDP nasu ya kai dala biliyan 12, wanda ya kai kashi 58 cikin dari na dukkan kasashe membobin kungiyar AU. Yankin zai kasance yanki mafi girma na yin ciniki cikin 'yanci a nahiyar Afirka, kana zai zama muhimmin kashi na yankin yin ciniki maras shinge na daukacin nahiyar Afirka da aka shirya kaddamarwa a shekarar 2017. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China