Kungiyoyin dai wadanda suka kunshi kasashen nahiyar 26, sun hada da COMESA ta yankin kudu maso gabashin nahiyar, da ta gamayyar yankunan Afirka ta Gabas ta EAC, da kuma kungiyar gamayyar raya kudancin nahiyar Afirka ta SADC.
Da yake tsokaci game da wannan kuduri, Jean Rigi, wani babban jami'in kasar Burundi da ke kula da harkokin kungiyar EAC, ya ce an gudanar da taron share fage kan aikin kafa yankin na ciniki cikin 'yanci ne a birnin Bujumbura na kasar Burundi a ran 4 ga watan Agustar nan. Kuma bisa ci gaban tattaunawar, ana sa ran fara aiwatar da wannan manufa ne a shekarar 2015 mai zuwa.
Mr. Rigi ya ce wannan shiri zai tallafa wa kasar Burundi matuka, sakamakon wurin da take a yankin. Baya ga kasancewar yankin ciniki cikin 'yancin wata babbar kasuwa, da za ta amfani mutane kimanin miliyan dari shida. (Maryam)