in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika za ta kaddamar da yarjejeniyar kasuwanci ta nahiyar a 2017
2015-06-11 11:16:50 cri

Kasashe mambobin tarayyar Afrika (AU) za su fara shawarwari kan wata yarjejeniyar shige da fice cikin 'yanci ta nahiyar (CFTA) da ke kunshe da dukkan kasashen Afrika, da zummar kara bunkasa kasuwanci a fadin shiyyar tsakanin kasashe 54 da ke cikin wannan kungiya, a cewar wani labari a ranar Laraba a birnin Johannesburg.

An samu ci gaba wajen kaddamar da wannan yarjejeniya ta yankin ta cinikayya cikin 'yanci na bangarori uku (TFTA) da aka kaddamar a Masar da ke kunshe da kasashen Afrika 26, in ji Fatima Haram Acyl, kwamishinar AU a fannin kasuwanci da masana'antu.

Yarjejeniyar TFTA ta kasance tamkar wani ginshiki domin kafa CFTA.

Madam Acyl ta yi magana ce yayin taron kungiyar AU karo na 25 da ke gudana a yanzu haka a birnin Johannesburg. Afrika ta Kudu na karbar bakuncin wannan taro da aka bude a ranar 7 ga watan Yuni har zuwa ranar 15 ga watan Juni, bisa taken "Shekarar wayewar mata da ci gaba zuwa ajandar shekarar 2063 a Afrika"

CFTA na daga cikin manyan batutuwan da za'a mai da hankali a kai tsakanin mahalarta wannan dandali.

An tsai da cewa, wannan yarjejeniya ta tsakanin kasashen Afrika, idan aka sanya mata hannu a yayin wannan taro, zai kai ga amince da CFTA nan da shekarar 2017, a cewar madam Acyl.

CFTA da aka gabatar za ta zama wani muhimmin abu na dabarar AU domin kara bunkasa kasuwanci a cikin shiyyar da a kalla kashi 50 cikin 100 a tsawon shekaru goma masu zuwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China