Ran 23 ga wata, ofishin kula da harkokin tattalin arziki da cinikayya na karamin ofishin jakadancin Sin da ke Lagos ya ruwaito kididdigar da hukumar kwastan ta Sin ta samar cewa, yawan hajojin da Sin ta fitar zuwa kasar Nijeriya ya kai dallar Amurka biliyan 5.43, adadin ya karu da kashi 27.8 bisa dari bisa na bara, adadin ya haura saurin karuwar yawan hajojin da Sin ta ke fitarwa zuwa kasashen ketare wanda ya kai kashi 10.4 bisa dari. Bugu da kari, yawan hajojin da kasar Sin ta shigo daga kasar Nijeriya ya kai dallar Amurka miliyan 593, adadin ya ragu sosai idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. (Maryam)