Jakadan kasar Sin dake Jamhuriyar Tarayyar Najeriya mista Deng Boqing, ya bayyana a ranar Jumma'a 26 ga wata yayin da yake hira da wakilan wasu kamfanonin kasar Sin, cewa bisa kokarin gwamnatocin kasashen 2 a fuskar karfafa mu'amala tsakaninsu, an kara shigar da wasu fannoni cikin huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da bangarorin 2 suka kulla, inda hakan ya sa cinikayyar da ake yi tsakanin kasashen 2 ke samun karuwa.
A cewar jakada Deng, alkaluman da hukumar kwastam ta kasar Sin ta gabatar sun sheda cewa, kasar Najeriya ta zamo ta 3 a duniya a fuskar yawan cinikayya tare da kasar Sin, kana ta kasance kasuwa ta 2 da kasar Sin ta fi kai kayayyakinta.
Don haka, mista Deng ya kara karfafa gwiwar kamfanonin kasar Sin domin su yi amfani da wannan kyakkyawar dama ta fuskar hada kai tsakanin Sin da Najeriya, sa'an nan su yi tsintsiya madaurinki daya, wato suyi kokarin hada kai, ta yadda za a samu damar inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen 2 .
Karamin jakadan kasar Sin dake Najeriya mai kula da harkokin tattalin arziki da ciniki mista Zhou Shanqing ya ce, a farkon rabin shekarar bana, yawan cinikayyar da aka yi a tsakanin Sin da Najeriya ya kai fiye da dalar Amurka biliyan 6, inda wannan jimillar ta nuna karin kashi 18.8% bisa kwatankwacin lokacin bara. A cewar mista Zhou, tsarin tattalin arzikin kasar Najeriya da na kasar Sin na nuna cewar za su iya biya ma juna bukata, don haka kasar na son kara hada kai da kasar Sin. A sabili da haka, zuba jari a Najeriya zai sa a samu dama mai kyau, wadda za ta wuce kalubalen da za a fuskanta. (Bello Wang)