in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya kaddamar da wani shirin inganta cinikayyar kasa da kasa
2013-09-09 20:38:49 cri

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da wani shirin musaya da nufin bunkasa harkokin cinikayya tsakanin Najeriya da sauran kasashen duniya.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da 'yan Najeriya mazauna kasar Kenya a birnin Nairobi, babban birnin kasar. Inda ya ce shirin da ma'aikatar kula da harkokin masana'antu, cinikayya da zuba jarin Najeriya ta kirkiro, zai karfawa kanana da matsakaitan masana'antu na 'yan Najeriya da ke gida da waje gwiwa.

Ya ce shekaru biyu kacal da kafa hukumar kula da harkokin cinikayya da zuba jari tsakanin kasashen Najeriya da Kenya, kasashen biyu sun fara fito da matakan kara bunkasa harkokin cinikayya a tsakaninsu, matakin da har ya sa shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya amince da baiwa 'yan kasuwar Najeriya na hakika iznin shiga kasar wato Visa na shekaru 5 zuwa 10 ba tare da wani cikas ba, kamar yadda ya bayyana yayin rufe dandalin 'yan kasuwar Najeriya da Kenya a ranar Jumma'a.

A halin da ake ciki, yanzu haka, sassa masu zaman kansu na kasashen biyu, sun tsara wasu matakai na yin takara mai fa'ida tsakanin kasashen da kawo moriyar juna ta fuskar dangantakar cinikayya da zuba jari.

Shugaba Jonathan ya yi kira ga 'yan Najeriya mazauna Kenya, da su yi kokarin ganin harkar cinikayya tsakanin kasashen biyu ta inganta, sannan su hada kai da hukumomin da abin da ya shafa, musamman matan da ke Kenya da ke son shiga harkokin kasuwanci.

Shi ma ministan masana'antu, cinikayya da harkokin zuba jari na Najeriya, Olusegun Aganga, ya ce manufar shirin, ita ce baiwa 'yan Najeriya da ke ketare damar ba da tasu gudummawar wajen bunkasa harkokin fitar da kayayyakin kasar da ba su da alaka da man fetur.

A sakamakon tattaunawar da aka yi tsakanin sassa masu zaman kansu na kasashen biyu, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, wanda ya jagoranci 'yan kasuwar Najeriya, ya yi wa mahalarta dandalin jawabi, inda ya sanar da zuba jarin Dala miliyan 400 a bangaren samar da siminti na kasar Kenya.

A jawabansu shugabannin kasahen Najeriya da Kenya, sun bayyana cewa, an samu cikakkiyar nasara yayin musayar ra'ayoyi tsakanin 'yan kasuwar kasashen biyu, kuma wannan wata alama ce ta samun nasara ga kasashen biyu. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China