in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harkokin cinikayya sun inganta a Afirka ta Kudu
2013-05-16 10:09:38 cri

Cibiyar harkokin kasuwanci da masana'antu ta kasar Afirka ta Kudu ta sanar ranar Laraba cewa, harkokin cinikayya a kasar sun bunkasa fiye da yadda ake tsammani a cikin watan da ya wuce zuwa matsayi da aka gani tun watan Maris na shekarar 2012.

Ma'aunin harkokin cinikayyan ya haura da maki biyar wato daga 51 a watan Fabrairu zuwa 56 a watan Maris na shekarar 2013, kana ya sake haurawa da maki biyar zuwa 61 a watan Aprilun 2013, in ji cibiyar.

Ma'aunin da a kan sabunta lokaci-lokaci ya haura da maki 11 zuwa 65 a watan Aprilun 2013, wato daga 54 a watan Maris na 2013, inda hakan ya nuna cewa, bunkasar ba wai na irin wanda aka saba gani ba ne ko kuma na hasashen dogon lokaci.

Cibiyar ta ci gaba da cewa, an samu bunkasar ne saboda tsawon lokacin karshen mako, daga watan Maris zuwa Aprilu a 2013, kuma harkar cinikin motoci ya samu bunkasa a watan Aprilun 2013 kamar yadda adadin cinikayyar ya nuna.

A cikin watan Maris, an gano cewa ma'aunin ya nuna saukowar harkoki a watan Maris 2013 da maki 4 fiye da na watan Maris 2012, to amma ma'aunin ya nuna cewa, na watan Aprilu 2013 ya haura da maki 13 fiye da na watan Maris 2012.

Duk da wannan ci gaban da aka samu tsakanin watannin Maris da Aprilu, harkokin cinikayya sun haura ne da maki 2 a watannin hudun farko na 2013 idan aka kwatanta da na wannan lokaci a 2012.

Cinikayya da bukatar kayayyaki da suka haura da maki 10 da 8 daki daki a watan Aprilu 2013 su ne suka haifar da bunkasar da ma'aunin ya nuna a watan Aprilu 2013.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China