Kokarin kafa wani yankin ciniki cikin 'yanci a nahiyar Afrika na bisa hanya, kuma kasashen na cigaba da daidaita tsarin siyasa da na dokoki domin cimma wannan buri, in ji komishinar kungiyar AU ta fuskar kasuwanci da masana'antu, madam Fatima Haram Acyl.
Kasashen Afrika sun kafa wasu hukumomi na cikin gida domin bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen Afrika, da kuma tabbatar da shige da ficen al'ummomin wadannan kasashe.
Wannan mataki zai gaggauta babban sauyi ga masana'antu a nahiyar Afrika, in ji madam Acyl a yayin babban taron ministocin kungiyar AU a birnin Malabo na kasar Guinea-Equatorial.
Madam Acyl ta bayyana a yayin taron manema labarai cewa, kasashen Afrika sun amince kawar da shingayen dake dakatar da musanya a kan iyakokin kasashen, da ma shawagin mutanen dake da kwarewa.
Kafa wannan yankin ciniki cikin 'yanci na daga cikin jadawalin 2063 da kasashen mambobin kungiyar tarayyar Afrika AU suka tsara a shekarar 2013 domin aza tunbalin hangensu bisa shekaru hamsin masu zuwa. (Maman Ada)