Kasashen nahiyar Afirka sun bayyana aniyarsu ta kaddamar da yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci tsakanin kasashen da ke nahiyar (CFTA) yayin taron kolin kungiyar tarayyar Afirka ta AU da za a gudanar a tsakiyar watan Yunin wannan shekara.
Batun bullo da yarjejeniyar ciniki cikin 'yancin tsakanin kasashen da ke nahiyar shi ne abin da za a tattauna a yayin taron kolin kungiyar karo na 25 da aka shirya gudanarwa daga ranar 14-15 ga watan Yunin wannan shekara a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
Minista a fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu Jeff Radebe wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a birnin Cape Town, ya kuma bayyana cewa, ana sa ran idan har aka kaddamar da wannan yarjejeniya, za ta samar wa sama da mutane miliyan 1.3 aikin yi baya ga karuwar GDP da ta kai sama da dala tiriliyan 2.
Radebe ya ce, wannan yarjejeniya za kuma ta kara ninka yankunan ciniki cikin 'yanci da ke nahiyar har sau uku baya ga bunkasa harkokin tattalin azrikin al'ummomin da ke shiyyar.
Bugu da kari, za ta baiwa kananan 'yan kasuwa da masu zuba jari damar raya kasuwanni, tare da bullo da hanyoyin cinikayya a nahiyar. (Ibrahim)