in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga kasashen Afirka da su amince da sabuwar yarjejeniyar cinikayyar makamai
2014-06-05 15:18:04 cri

Kungiyar gamayyar majami'u ta duniya WCC, ta yi kira ga daukacin kasashen Afirka, da su amince da sabuwar yarjejeniyar cinikayyar makamai ta ATT, dokar da a cewar WCCn, da zarar ta fara aiki, za ta taka muhimmiyar rawa, wajen dakile yaduwar makamai ba bisa ka'ida ba.

Cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin Nairobin kasar Kenya, WCCn ta bayyana irin ci gaban da wannan kuduri ke samu kawo wannan lokaci. A cewar Joseph Dube na kungiyar ta WCC, daukacin masu ruwa da tsaki na daukar dukkanin matakan da suka wajaba, wajen ganin sabuwar yarjejeniyar ta samu karbuwa yadda ya kamata.

Ita dai wannan sabuwar yarjejeniyar kasa da kasa ta tanaji ka'idojin musayar makamai tsakanin kasashen duniya daban daban.

Yanzu haka dai WCC na ci gaba da zawarcin karin kasashe 25, wadanda sai sun sanya hannu kan wannan yarjejeniya, za a kai ga samun kaiwa ga rabin adadin yawan kasashen da ake nema domin aiwatar da dokar.

Tuni dai Najeriya, da Mexico, da Finland, da Norway, da Jamus, da kuma Birtaniya suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China