Sanarwar da gwamnatin Kenya ta bayar a wannan rana ta nuna cewa, kafa wannan yankin ciniki mai 'yanci zai taimaka ga inganta harkokin ciniki a tsakanin sassan gabashin Afirka da na tsakiyar Afirka da kuma na kudancin nahiyar. Har ila yau, 'yan kasuwa da ke kasar da sauran sassan shiyyar za su iya sayen kayayyakin da suka ga dama a wannan yankin ba tare da zuwa kasashen hadaddiyar daular larabawa da Sin ko Japan da a baya suka saba ba.
An ce, gwamnatin Kenya ta kebe filin da fadinsa ya kai muraba'in kilomita 3400 domin kafa yankin, wanda ya hada da muraba'in kilomita 2000 da ke Mombasa.(Lubabatu)