Shugaba Essebsi ya ba da jawabi ta gidan talabijin cewa, ana fuskantar kalubalen ta'addanci a kasar, a hakika, kasar na cikin halin yaki a yanzu, shi ya sa, ya kamata gwamnatin kasar ta dauki matakai yadda ya kamata domin fuskantar wannan kalubale.
Kaza lika, bisa dokokin kasa ta Tunisiya, an ce, za a kara mulki ga gwamnati da kuma 'yan sandan kasar, yayin da ake cikin halin dokar ta baci a kasar, amma, za a hana ikon taron jama'a da dai sauran batutuwan da abin ya shafa a kasar a wannan lokacin. Kana, kafin a sanar da dokar ta baci a kasar, gwamnatin kasar ta riga ta aike da karin 'yan sanda zuwa wuraren yawon shakatawa na kasar.
A ran 26 ga watan da ya gabata, dakaru masu tsattsauran ra'ayi sun kai hari a wani otel dake birnin Sousse na kasar Tunisiya, wanda ya haddasa mutuwar mutane guda 38, wadanda galibinsu 'yan kasar Burtaniya. Daga bisani kuma, kungiyar mai tsattauran ra'ayi ta IS ta sanar da daukar alhakin harin din. (Maryam)