Bisa wannan shirin, dakarun kasar Aljeriya na kara rubanya ayyukansu na bincike da sanya ido kan tashohin binciken jama'a da motoci domin kawar da duk wani yunkurin kutsa kan 'yan ta'addan da suka fito ko suke son shiga kasar Tunisiya.
A ranar Jumma'a ce, wani mutum ya bude wuta kan masu yawon shakatawa dake bakin ruwa da kuma wuraren ninkaya na gidan otel din Riu Imperial Marhaba dake Port El Kantaoui, kusa da Sousse (mai nisan kilomita 140 daga kudancin birnin Tunis), a arewa maso gabashin kasar Tunisiya.
Alkaluman baya baya sun nuna cewa mutane 39 aka kashe yayin 39 suka jikkata, kuma yawancinsu 'yan kasashen waje ne, in ji wata majiyar ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Tunisiya a ranar Asabar.
Kasashen Aljeriya da Tunisiya sun rattaba kan yarjeniyoyin dangantaka a fannin yaki da ta'addanci. (Maman Ada)