A ran 26 ga wata da dare, a hukunce ne sabon firaministan Tunisiya Mehdi Jomaa ya gabatar da sunayen sabuwar gwamnatinsa ga shugaban kasar Moncef Marzouki, sabuwar gwamnatin dake kunshe da ministoci 21 da sakatarori 7.
Mista Jomaa ya yi nuni cewa, yana fatan wannan sabuwar gwamnati za ta zama gwamnatin wucin gadi ta karshe har zuwa babban zaben da za a shirya a kasar, sabuwar gwamnatin za ta share fage ga babban zabe, da kago wani yanayi mai kyau ga babban zabe. Haka zalika, mista Jomaa ya bayyana cewa, kila sabuwar gwamnatin wucin gadi da yake shugabanta ba ta iya samu goyon baya daga dukkan jam'iyyun siyasa na kasar ba, amm yana fatan jama'ar kasar Tunisiya za su nuna goyon baya gare shi da gwamnatinsa. (Danladi)