Sanarwar ta bayyana cewa, a wannan ranar 'yan sandan kasar sun kama mutane 21 da aka zarge su da aikata laifin kai harin, wadanda su ne membobin kungiyoyi biyu na dakaru a kasar. Ya zuwa yanzu, an riga an kama dukkan mutanen 46 dake da nasabaalakar kai tsaye da harin ta'addanci da aka kai ga dakin ajiye kayayyakin tarihi na Bardo kai tsaye.
A ranar 18 ga watan Maris, an kai hari ga dakin ajiye kayayyakin tarihi na Bardo a kasar Tunisia, wanda ya haddasa mutuwar mutane 23, yayin da mutane fiye da 40 suka ji rauni. (Zainab)