Shugabar kwamitin kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma ta nuna rashin jin dadi ga harin ta'addanci da aka kai ga dakin adana kayayyakin tarihi na Bardo dake kasar Tunisia a Laraba, ta bayar da sanarwa cewa, kwamitin kungiyar AU ya yi tir da wannan harin ta'addanci, da jajantawa iyalan mutanen da suka mutu a sakamakon harin, da gwamnati da jama'ar kasar Tunisia.
Kana Madam Zuma ta yi kira ga jama'a da gwamnatin kasar Tunisia da su yi kokarin tabbatar da demokuradiyya da zaman lafiya a kasar.
Ban da wannan kuma, shugabar kwamitin na AU ta jaddada cewa, harin ta'addanci da aka kai ga Tunisia ya nuna cewa, ana bukatar kasashen Afirka da su kara yin hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi. (Zainab)