Sama da al'ummar kasar miliyan 5 da dubu dari 3 ne dai ake sa ran zasu kada kuri'un su, domin zabar ko dai Beji Caid Essebsi mai ra'ayin 'yan ba ruwan mu daga jam'iyyar Nidaa Tounes, ko kuma shugaban kasar na yanzu Moncef Marzouki na jam'iyyar masu ra'ayin Islama ta Ennahda.
A zagayen farko na zaben Mr. Essebsi ne ya lashe mafiya yawancin kuri'un da aka kada, da kason 39.46 bisa dari, ya yin da Marzouki ke biye da kaso 33.43 bisa dari.
Tuni dai 'yan kasar dake kasashen waje suka fara kada na su kuri'u tun a ranar Alhamis, za kuma a ci gada da zaben har zuwa wayewar garin Litinin. Hukumar zaben kasar ta ce za ta sanar da sakamakon fari, na wannan zagayen zabe a goben.