in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi maraba da yadda aka gudanar da babban zaben Tunisia lami lafiya
2014-12-24 21:00:57 cri
A yau Laraba 24 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin madam Hua Chunying ta bayyana a gun taron manema labaru cewa, Sin ta yi maraba da yadda aka gudanar da babban zabe a kasar Tunisia lami lafiya.

A ranar 22 ga wata, babban kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar Tunisia ya gabatar da sakamakon babban zabe a zagaye na biyu, inda shugaban jam'iyyar "Call of Tunisia" Beji Caid Essebsi ya lashe zaben.

Madam Hua ta bayyana cewa, Sin na fatan Tunisia za ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da habaka a kasar cikin dogon lokaci, da fatan yin kokari tare da ita domin sa kaimi ga bunkasa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.

An bada labarin cewa, a ranar 22 ga wata, babban kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar ya shelanta cewa, Beji Caid Essebsi ya lashe babban zaben a zagaye na biyu bisa kuri'u kashi 55.68%, a don haka, ya kasance zababben shugaba na farko bayan da aka yi juyin juya hali a kasar a shekarar 2011.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China