Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya ce har kullum kasar Sin na adawa da kowane irin aiki na ta'addanci, tana kuma Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa fararen hula da ba su ji kuma ba su gani ba.
Mr. Hong ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, biyowa bayan harin da aka kai a gidan adana kayan tarihi dake Bardo a tsakiyar birnin Tunis, fadar mulkin kasar Tunisiya, harin da kuma ya hallaka mutane 22, yayin da kuma wasu 50 suka jikkata.
Hong Lei ya kara da cewa, kasar Sin na ganin cewa kamata ya yi kasashen duniya su kara kyautata hadin gwiwarsu wajen magance barazanar ta'addanci, bisa muhimman ka'idojin da aka tanada cikin kundin tsarin MDD, da sauran manyan ka'idoji masu alaka da huldar da dake tsakanin kasa da kasa. (Tasallah Yuan)