Ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Tunisiya Mongi Hamdi, ya soki lamarin tsoma hannun kasashen wajen cikin rikicin kasar Libiya.
Mr. Hamdi wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labaru, gabanin bude taron karawa juna sani na shekara-shekara na tawagogin ma'aikatan diflomasiyya, ya ce komawa teburin shawara ne kadai zai bada damar warware rikicin kasar ta Libiya.
A ranar 14 ga watan Yulin da ya shude ne dai ma'aikatar wajen kasar ta Tunisiya, ta jagoranci taron takwarorinta dake makwabtaka da Libiya, domin tattauna hanyoyin magance matsalolin tsaro a Libiyan. Taron da ya bada damar kafa kwamitocin tsaro da na siyasar kasar.
Wadannan kwamitoci biyu a cewar Hamdi sun riga sun fara zama, suna kuma musayar bayanai da kasar ta Tunisiya game da ci gaban da ake samu.
A cewar Mr. Hamdi dole ne a ci gaba da hadin gwiwa da mahukuntan kasar Libiya, wajen yakar 'yan ta'adda, wadanda ya ce na zama barazana ga daukacin yankin baki daya.(Saminu Alhassan)