in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Tunisiya ya gabatar da takardarsa ta yin murabus
2014-01-10 10:19:40 cri

A ran 9 ga wata da yamma bisa agogon wurin, firaministan kasar Tunisiya Ali Laarayedh ya gabatarwa shugaban kasar Moncef Marzouki da takardarsa ta yin murabus daga mukaminsa, wanda a wannan rana zai ba da izni ga sabon firaminista Mehdi Ben Jomaa da ya kafa wata sabuwar majalisar ministoci.

A gun taron da aka shirya tsakanin shugaban kasar Marzouki da shugaban majalisar tsara kundin mulki Mustapha Ben Jaafar a ran nan da safe, Ali Laarayedh ya nuna aniyarsa ta yin murabus, inda ya ce, murabus dinsa ya shaida cewa, gwamnatin da ya jagoranta ta cika alkwarinta, ta bi shirin daidaita rikicin da ya kuno kai a babban taron tattaunawa na kasar. Ya kara da cewa, murabus din da ya yi zai gaggauta shirin mika mulki na kasar ta Tunisiya.

Tun bayan da aka yi wa wani 'dan majalisa daga jam'iyyar da ke adawa da gwamnati Mohamed Brahmi kisan gilla a ranar 25 ga watan Yuli na bara, Tunisiya ta shiga cikin rikicin siyasa mai tsanani, inda aka dakatar da shirin komawa kasar ga mulkin dimokuradiyya. Bayan haka kuma, gamayyar kungiyoyi kwadago na kasar guda hudu sun shirya babban taron tattaunawa a duk fadin kasar, bayan shawarwarin da suka yi cikin watanni da dama, kungiyoyin sun shiga zaben da aka yi a ranar 14 ga watan Disamba, inda suka zabi Mehdi Ben Jomaa a matsayin firaministan gwamnatin wucin gadi na kasar ta Tunisiya.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China