A safiyar wannan rana, a karkashin jagorancin shugaban kasar Tunisia Beji Caid Essibsi, jama'ar kasar fiye da dubu daya da shugabannin kasashen duniya da suka nuna goyon baya ga kasar sun yin zanga-zanga tun daga unguwar Bab Saadoun zuwa wurin ajiye kayayyakin tarihi na Bardo.
Bayan da masu zanga-zangar suka isa wurin ajiye kayayyakin tarihi na Bardo, shugaba Essibsi ya shugabanci bikin tunawa da mutanen da suka mutu a sakamakon harin da aka kai ga wurin Bardo, kana ya yaye gyalle a kan kabarin su. Essibsi ya bayyana cewa, an yi zanga-zangar ne don nuna cewa, jama'ar kasar Tunisia ba sa jin tsoron ta'addanci, kuma ba su kadai ba ne ke yaki da shi. (Zainab)