Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Tunisiya, a yammacin ranar 29, ta sanar da sakamakon zabe dake bayyana mista Beji Caid Essebsi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Tunisiya.
A cewar hukumar zaben Tunisiya, mista Beji Caid Essebsi ya lashe zaben da kashi 55.68 cikin 100 na kuri'un da aka jefa, yayin da abokin takaransa Moncef Marzouki shugaba mai barin gado ya samu kashi 44.32 cikin 100 na kuri'un da ake jefa.
Beji Caid Essebsi mai shekaru 88 a duniya zai yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Tunisiya a ran 31 ga wata, wanda kuma zai kasance shugaban kasar Tunisiya na biyar, kana shugaba na farko da jama'ar kasar suka zaba bayan juyin juya halin da aka yi a kasar a shekarar 2011. (Amina)