A ranar 18 ga wata, dakaru dauke da makamai sun yi garkuwa da mutane a gidan adana kayan tarihi na Bardo da ke kusa da babban dakin majalisar dokokin Tunisiya, daga bisani kuma, ma'aikatar tsaro ta kasar ta tashi tsaye don kubutar da mutanen, lamarin da ya janyo musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da dakarun 3. Ya zuwa wannan rana da yamma, an kawo karshen lamarin. Bisa labarin da aka bayar, an ce, a cikin mutane 22 da suka mutu, ciki har da masu yawon bude ido 20, wadanda suka fito daga Tunisiya, Faransa, Poland, Italiya da sauransu.
A wannan rana da yamma, shugaban kasar Tunisiya Beji Caid Essebsi ya yi jawabi ta gidan talibijin domin janjanta wa iyalan mutanen da suka mutu, ciki har da 'yan gida da masu bude ido na kasashen waje, kuma ya nuna godiya ga kasashen waje da dama da suka nuna goyon baya ga jama'ar Tunisiya a kan lamarin. Tare da yin alkawari ga jama'ar kasar Tunisiya cewa sai ya ga karshen tsagerun da ke namen janyo fitina ga kasar.
Sakatare janar na M.D.D. Ban ki-moon ya ba da wata sanarwa ta kakakinsa, inda ya yi kakkausar suka game da harin da aka kai a gidan adana kayan tarihi na Bardo a kasar Tunisiya, tare da nuna juyayinsa game da mutanen da suka rasa rayukansu a cikin lamarin.(Bako)