in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da sabon shugaban kasar Tunisiya
2014-12-31 20:45:03 cri
A yau da safe ne, Beji Caid Essebsi ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Tunisiya a yayin taron wakilan jama'ar kasar, lamarin da ya nuna cewa, wa'adin aikinsa na shugaban kasar na shekaru biyar ya fara a hukunce.

A yayin bikin rantsuwar, Mr. Essebsi ya nuna godiyarsa matuka ga dukkanin magoya bayansa, da wadanda suka zabi Moncef Marzouki, sa'an nan kuma, ya ce, kyakyyawar makoma ga jama'ar kasar tana tafe sakamakon kawo karshen babban zaben shugaban kasar, kana, ya yi alkawarin cewa, zai kiyaye tare da bi tsarin mulkin kasar yadda ya kamata, ya kuma yi alkawarin gudanarwar harkokin mulki ba tare da wata rufa-rufa ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China