in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Tunisiya ya sanar da kawar da dokar ta baci
2014-03-07 10:41:25 cri

Fadar shugaban kasar Tunisiya ta bayar da wata sanarwa a ran 6 ga wata da ke cewa, shugaban kasar Moncef Marzouki ya sa hannu kan umurnin gwamnati na dakatar da dokar ta baci da aka kafa a fadin kasar tun a farkon shekara ta 2011, bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Zine el-Abidine Ben Ali.

Sanarwar ta ce, shugaba Marzouki ya yanke wannan shawara ce bayan da ya yi shawarwari da firaminista Mehdi Ben Jomaa da shugaban majalisar tsara tsarin mulki Mustapha Ben Jaafar da kwamitin kula da harkokin tsaro na kasar. Sanarwar ta jaddada cewa, kawar da dokar ta bacin ba za ta yi tasiri kan 'yan sanda da ke gudanar da ayyukansu ba, kuma duk lokacin da aka samu wata bukata, za a nemi taimako daga sojoji.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China