Sin ta nuna rashin jin dadi kan rikicin da ya rutsa da shagunan kasar Sin a Kongo Kinshasa
Game da rikicin da ya rutsa da shagunan kasar Sin a Kongo Kinshasa a kwanan baya, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying a ranar alhamis 22 ga wata, ta nuna matukar rashin jin dadin ta a kan hakan, tare kuma da neman kasar da ta dauki matakin da ya dace don ba da kariya ga hukumomin kasar Sin da ma Sinawa dake kasar.
Ban da haka, ta kara da cewa, bayan faruwar rikici, ofishin jakadancin kasar Sin dake Congo Kinshasa ya dauki mataki cikin gaggawa ya kuma hada kai da Sinawa dake kasar da 'yan sandan kasar don tinkarar rikici tare, ta yadda za a kiyaye lafiyar Sinawa dake wurin da ba da taimako da ya wajaba. Kakakin na sin ta ce, kasar na fatan maido da kwanciyar hankali a kasar ta Congo Kinshasa cikin sauri . (Amina)