in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan tawayen M23 sun fice daga Goma
2012-12-02 16:32:49 cri
A ranar Asabar ne 'yan tawayen M23 da ke Jamhuriyar Demokiradiyar Congo suka janye daga Goma, babban birnin lardin arewacin Kivu.

Wata sanarwar da sojan Uganda ta bayar, ta bayyana cewa, 'yan tawayen sun kammala janyewa daga Goma da Sake inda gwamnati ta maido da kula da hukumomi.

Kasar Uganda ce ta gudanar da taron shugabannin kasa da kasa game da yankin Great Lakes mai mambobi 11.

'Yan tawayen sun janye daga yankin na Goma ne bayan taron shugabannin a makon da ya gabata, inda aka tsara wasu matakan tilasta musu janyewar, a wani mataki na daidaita lamarin.

Kungiyar ta M23 dai ta shiga Goma ne kwanaki goma da suka gabata, a wani mataki na mayar da martani ga kin amincewar Kinshasa na yin tattaunawa kai tsaye da kungiyar da ta shafe tsawon wata guda tana tayar da kayar baya.

Tawagar MDD da ke Jamhuriyar demokiradiyar Congo ta cimma yarjejeniya da kungiyar ta M23 game da wasu batutuwa kafin 'yan tawayen su kammala janyewa a ranar Asabar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China