in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan adawa a Kongo Kinshasa ta amince da janye sojojinta daga birnin Goma.
2012-11-28 10:18:57 cri
Ranar 27 ga wata, sojojin kasar Uganda sun nuna cewa, rundunar 'yan adawa da gwamnatin Kongo Kinshasa ta M23 ta yarda da janye sojojinta daga birnin Goma, hedkwatar lardin Arewacin Kivu wadda ta kasance wata jiha dake da muhimmanci sosai a gabashin kasar Kongo Kinshasa.

A wannan rana a hedkwatar sojojin kasar Uganda dake Kampala babban birnin kasar, wani jigo na rundunar sojojin kasar Uganda Aronda Nyakairima bayan ganawarsa da wakilan sojojin kasashen Kongo Kinshasa, Uganda da Ruwanda da shugabannin M23 da ta gudana a daren ranar 26 ga wata, ya ce, shugabannin M23 sun yarda da janye sojojinsu daga birnin Goma cikin sa'o'i 48 tun daga ran 27 ga wata. Kuma Aronda Nyakairima zai sa ido kan wannan aiki.

Amma, a wannan rana, rundunar ta M23 ta sanar da cewa, za ta janye sojojionta bisa wani sharadi guda, wato shugaban Kongo Kinshasa Joseph Kabila Kabange ya yarda da aiwatar da yin shawarwari, tare da sakin wadanda suka aikata laifuffukan siyasa, tare da tarwatsa hukumar zabe da sauransu. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China