Bisa kudurin da aka cimma, kwamitin sulhu na M.D.D ya bukaci dukkanin kasashen duniya da su toshe dukkan wata kafa da za a iya amfani da ita ta jiragen sama, da na ruwa, don samar, ko sayar, ko kuma musayar makamai da harsashi ga kungiyoyi da jama'a masu zaman kansu da suke aiki a kasar Kongo(kinshasa). A kuma hana ba da shawara da ke da nasaba da koyar da dabarun soja, da ba su kudade ko tallafi da dai sauransu.
Ban da wannan kuma, kudurin ya bukaci 'yan tawayen M23 da sauran kungiyoyin 'yan tada kayar baya da su dakatar da tashe-tashen hankula da su iya kawo cikas ga zaman lafiyar kasar.(Bako)