in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar farko ta rukuni na 15 na sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin dake zuwa kasar Congo Kinshasa ya tashi
2012-11-28 10:06:57 cri
A ranar 27 ga wata, tawagar farko na rukunin 15 na sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin ta tashi daga birnin Xi'an na kasar Sin zuwa kasar Congo Kinshasa don karbar aiki a yankin.

Rukunin 15 na sojojin ya kunshi rassan sojojin injiniyoyi da na kiwon lafiya da yawansu ya kai 218. Bayan da aka horar da su har na tsawon watanni 3, sojojin sun samu kwarewa kan aikin kiyaye zaman lafiya, tabbatar da tsaro da kuma kiwon lafiya, Za su gudanar da ayyuka har na tsawon watanni 8 a yankin.

Tawaga ta biyu ta rukunin za ta tashi a farkon watan Disamba, inda za a kammala karbar aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Congo Kinshasa a wannan karo. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China