Gwamnatin Congo tana cigaba da tattauna hanyar ganin a zuba sojojin kasa da kasa da su shiga tsakani a yankin Kivu in ji mista Baleke, sannan ya kara da cewa wadannan ayyukan alla wadai dake faruwa a daidai wannan lokaci da muke nuna niyyarmu ta warware wannnan rikici cikin ruwan sanyi.
A cewar kakakin M23, gwamnatin Kinshasa na neman kara samun lokaci kafin zuwan wadannan sojojin kasa da kasa dubu hudu, wadanda za a ba su nauyin sa ido a kan iyakar RDC-Congo da Rwanda da kuma farautar 'yan tawayen M23 dake gabashin kasar RDC-Congo.
Yan tawayen M23 sun amince da tsagaita bude wuta a ranar 8 ga watan Janairun da ya gabata a yankin Arewacin Kivu da kuma gabashin RDC-Congo. (Maman Ada)