in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalissar ministocin tsaron kasashen Kudancin Afirka ta bukaci sauya rundunar MDD dake Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo
2013-01-24 09:39:22 cri
Taron mambobin majalisar ministocin tsaron kasashen kudanci da na yankunan babban tafkin nahiyar Afirka, ya bayyana bukatar sauya rundunar samar da zaman lafiya ta MDD dake gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, wata runduna daga nahiyar. Ministan tsaron kasar Uganda Janar Aronda Nyakairima ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai ranar Laraba 23 ga watan nan, yana mai cewa taron kungiyar bunkasa yankin wato ICGLR ya yanke shawarar mika wannan bukata ne ga kungiyar AU, bayan zaman tattaunawar da ya yi a karshen makon jiya, duba da yadda a cewar mahalarta taron, tawagar ta MDD ta gaza, wajen kare fararen hula dake kasar ta Congo Kinshasa. "Muna mika wannan kuduri dake nuna bukatar dake akwai ta baiwa kasashen Afirka damar karbar aikin da MONUSCO ke yi a jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ga kungiyar AU, zai fi kyau mu samar da runduna, su kuma su ba mu tallafi domin tabbatar da nasarar da ake fata, ganin yadda dakarun nahiyar tamu ke da kwarewa wajen gudanar da irin wannan aiki, sabanin abin da ake gani a yanzu daga dakarun kasashen waje," a ma'anar kalaman Janar Nyakairima. Daga nan sai Ministan tsaron kasar ta Uganda ya bayyana cewa tuni suka shirya mika wannan bukata ga taron kungiyar ta AU da ke tafe a karshen makon nan, wanda aka kuma tsara gudanarwa a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. (Saminu Alhassan)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China