in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kongo Kinshasa ta karbi 'yan gudun hijira kimanin 3300 daga Afrika ta tsakiya.
2013-12-18 15:35:31 cri

Hukuma mai lura da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD, ta ce 'yan gudun hijira daga Afirka ta tsakiya, da yawansu ya kai kimanin 3300 sun tsallaka kasar Kongo Kinsha cikin watan Disambar wannan shekara kadai.

Wani jami'in hukumar ya bayyanawa manema labaru cewa, 'yan gudun hijirar sun bar gidajensu ne sakamakon rigingimun baya bayan nan dake addabar kasar. An ce hukumomin da wannan batu ya shafa sun yi rajistar wadannan mutane, kuma tuni aka bayyana bukatar samar da karin kayayyaki ba da tallafi domin tsugunar da su.

Bisa kididdigar da hukumar ta fitar, an ce har yznu, sansanonin 'yan gudun hijira 4, da kasar ta Kongo Kinsha ta kafa a lardunan Equateur da Orientale sun riga sun karbi 'yan gudun hijirar kasar Afrika ta tsakiyar fiye da 47000. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China