in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin yankin mahimman tabkuna sun fitar da wani shiri na janyewar 'yan tawaye a Jamhuriyar Demokradiya ta Kongo
2012-11-25 17:02:11 cri
Shugabannin kasashen muhimman yankunan tabkuna na Afrika a jiya Asabar 24 ga wata suka kammala taron gaggawa na yini daya, inda suka fitar da wani shiri ga 'yan tawayen M23 na janyewa daga garin Goma, yankin dake cikin birnin arewacin Kivu a gabashin kasar Jamhuriyar Demokradiya ta Kongo.

Shugabannin a cikin sanarwar bayan taron da suka fitar a Kampala babban birnin kasar Uganda sun ce, tilas ne 'yan tawayen M23 su dakatar da fadada yakin da suke kokarin yi, kuma su daina maganar son juyin mulkin halaltaciyar gwamnatin da aka zaba.

" M23 su janye daga sansanin da suke a yanzu zuwa wuraren da baya da babban matsayi na a kalla fiye da kilomita 20 daga arewa da garin Goma" inji sanarwar.

Shugabannin wadanda suka amince da cewa, a babban filin jiragen sama na garin Goma za'a zuba jami'an tsaro na 'yan ba ruwanmu, jami'an tsaro na gwamnatin Jamhuriyar Demokradiya ta Kongo da kuma jami'an 'yan tawayen M23, sun kuma amince da zuba bataliya daya kowanne na jami'an sojin jamhuriyar demokradiya ta kongo da kuma 'yan sandanta a garin Goma.

Kwamitin tsaro ta MDD zai samar da jami'an tsaro a shiyyar kungiyar 'yan ba ruwanmu da kuma wuraren da 'yan tawayen M23 ke rike da shi, inji shawarar da shugabannin suka bayar a cikin takardar.

Shi dai shirin janyewa 'yan tawayen za'a yi shi ne karkashin sa idon manyan hafsan sojojin kasashen Rwanda da jamhuriyar demokradiya ta Kongo, wanda babban Hafsan sojojin kasar Uganda zai jagoranta.

Kafin wannan dai kungiyar 'yan tawayen sun ki amincewa da umurnin shugabanin da su janye daga yankin Goma suna masu shan alwashin cigaba da yin fada idan har gwamnatin DRC ba ta nemi sulhu da su ba.

Su dai Shugabannin a lokacin taron gaggawar sun bukaci gwamnatin Jamhuriyar Demokradiya ta Kongo da ta saurari kungiyar 'yan tawayen domin jin kokensu tare da warware matsalolinsu tare.

Wannan taron dai ya samu halartar Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni,na DRC Joseph Kabila, na Kenya Mwai Kibaki, na Tanzaniya Jakaya Kikwete da Shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afrika Madam Nkosazana Dlamini-Zuma.

Wakilan kungiyar Kasashen gabashin Afrika da na kudancin Kasashen Afrika su ma sun halarci taron.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China