Madam Hua ta kara da cewa, kasar Sin na fatan sassa daban daban da lamarin ya shafa za su warware rikici ta hanyar yin tattaunawa bisa tushen girmama da tabbatar da ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan kasa, ta kuma yi kira ga kasashen duniya da kungiyoyin shiyya-shiyya da su ci gaba da kokarinsu na sassauta al'amura a gabashin Congo(Kinshasa) da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yammaci da tsakiyar shiyyar Afirka. (Tasallah)