Sannan masu ruwa da tsakin sun bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin wani taro da suka gudanar a birnin Kampala fadar mulkin kasar Uganda. Inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yadda za a maida wadannan mutane zuwa kasar ta Kongo Kinshasa.
Har ila yau sun kuma sanar da cewa, za a yi kokarin lallashin mutanen da yawansu ya kai dubu 184 dake samun mafaka a Uganda a halin yanzu, domin su yarda da faran aikin mayar da su kasar ta su ta asali.
A nasu bangare Uganda da hukumar lura da 'yan gudun hijira ta MDD, za su gudanar da binciken jin ra'ayin jama'a tsakanin wadannan mutane, don mika wani rahoto ga Kongo Kinshasa a karshen watan Yuli mai zuwa. Kaza lika hukumar 'yan gudun hijirar ta alkawarta samar da motoci ga 'yan gudun hijirar dake da niyyar koma gidajen na su. (Bello Wang)