Kasar Uganda, makwabciyar jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo, wadda ke kokarin shiga tsakanin bangarorin kasar, ta ba da labarin cewa, gwamnatin kasar Kongo Kinshasa da dakarun M23 sun fara shawarwari ne a ranar 7 ga wata, batutuwa mafi muhimmanci da za a tattauna a kai, su ne yadda za a tsara wasu muhimman manufofi don gudanar da shawarwari, da wa zai sa ido kan batun shawarwarin.
A wajen taron shawarwarin, wani wakilin dake wakiltar kungiyar al'ummar jama'ar Kongo Kinshasa ya bayyana wa manema labaru cewa, abun da ya fi muhimmanci ga jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo shi ne zaman lafiya, don haka dole ne bangarorin 2 dake fada da juna su kwance damara domin gudanar da shawarwari. Wakilin ya kara da cewa, jama'ar kasar suna son zaman lafiya, domin suna fatan gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a gidajensu, sa'an nan yaransu su je makarantu ba tare da matsala ba. Ban da haka, ya bayyana niyyarsa ta samar da zaman lafiya da ci gaban al'ummar kasar. (Bello Wang)