Shirin wanda ya tanadi kudade da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 892.6 ya cimma bukatun mutane miliyan 3.9 a fadin kasar, wadanda suke fama da karancin abinci, cututtuka da yake-yake a wannan shekara, in ji sanarwar.
An bayyana cewa, kudaden za su taimaka wajen samar da tallafi a fannonin abinci, wuraren kwana, kariya da kuma shirin samar da ruwa da tsabtace muhalli don kare jama'a daga cututtukan dake da hadari ga rayuka kamar cholera da bakon dauro.
Shirin har wa yau na mai burin taimakawa mahukunta su inganta ayyukan amfanin jama'a har ma da ilmi. (Lami)