in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan jami'an Amurka, Birtaniya da Faransa sun bukaci hana jin karar makamai a Kongo Kinshasa
2012-11-27 10:02:16 cri

Ranar 26 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka Victoria Nuland ta sanar da cewa, wasu manyan jami'an kasashen Amurka, Birtaniya da Faransa suna shiga tsakani a kasashen Ruwanda, Uganda da Kongo Kinshasa, inda suka nemi rundunar dake adawa da gwamnati ta M23 da sojojin gwamnatin kasar Kongo Kinshasa da su tsagaita bude wuta.

Yayin jawabi ga manema labaru da ma'aikatar harkokin waje ta saba yi, Victoria Nuland ta ce, mataimakin ministan harkokin waje mai kula da harkokin nahiyar Afrika Johnny Carson da wasu jami'ai masu kula da harkokin Afrika na kasashen Birtaniya da Faransa sun gana da shugabanni da manyan jami'an kasashen Ruwanda, Uganda da Kongo Kinshasa kwanan baya, inda suka yi kokarin warware rikice-rikice da suka barke a wadannan wurare cikin lumana kuma na dogon lokaci.

Bugu da kari, Victoria Nuland ta nanata matsayin da Amurka ta dauka kan lamarin, wato neman Kongo Kinshasa ta tabbatar da tsagaita bude wuta nan take, sannan rundunar ta M23 ta yi baya ta koma zuwa wurin da ta tsaya kafin watan Yulin bana. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China