in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin yankuna 10 za su hadu a kasar Uganda domin tattauna rikicin Jamhuriyar Demokradiya ta Kongo
2012-11-24 16:57:10 cri
Kamfanin dillancin labarai ta kasar Sin ta samo mana labari cewa a kalla shugabannin daga yankuna 10 na muhimman tabkunan ne za su hadu a Kamfala, babban birnin kasar Uganda a yau Asabar 24 ga wata domin tattaunawa game da rikicin dake wanzuwa a kasar Jamhuriyar Demokradiyya na Kongo da zummar kawo karshen shi tun bai kazanta ba, in ji wani babban jami'in gwamnati a jiya juma'a.

Henry Okello Oryen, ministan kasa na harkokin kasashen waje ya sheda ma Xinhua ta wayar tarho cewa, shugabannin karkashin kungiyar yankunansu, babban taron kasa da kasa na yankunan muhimman tabkunan za su yanke shawarar karshe game da shirin da suke da shi na aika sojoji 4000 a kasar sakamakon fadawar Goma, babban cibiyar a arewacin Kivu ga hannun 'yan tawaye a ranar Talatar da ta gabata.

Wannan taron dai na gaggawa da aka kira kwanaki uku bayan da shugaban kasar Joseph Kabila, shugaban kasar Rwanda Paul Kagame da na Uganda Yoweri Musaveni a ranar Larabar da ta gabata suka tattauna a kamfala domin samun hanyar kawo karshen wannan rikici wanda ya tilasta ma dubban jama'a daga kasar ta DRC yin gudun hijira zuwa kasashen Rwanda da Uganda dake makwabtaka da su.

Shuagabannin dai Museveni da Kabila da kuma Kagame a ranar Laraba suka yi kira ga 'yan tawayen da su fice daga garin Goma, wanda shi ne babban gari a gabashin kasar, kiran da 'yan tawayen suka yi watsi da shi.

Fada a gabashin kasar ya yi sanadiyyar rasa muhallin mazauna garin fiye da 475,000 ya kuma saka mutane 75,000 yin gudun hijira zuwa Uganda da Rwanda ,a cewar rahoton ofiishin ba da agajin gaggawa na MDD. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China