An yi bikin karbar tallafin abincin da Sin ta baiwa Saliyo a ranar Litinin 29 ga wata don taimakawa Saliyo wajen yaki da cutar Ebola. Ministan harkokin waje na kasar Saliyo da mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar, wakilin hukumar tsara shirin abinci ta duniya wato WFP kuma jakadan kasar Sin dake Saliyo Mr Zhao Yanbo, da mai bada shawara kan harkokin kasuwanci a ofishin jakadanci na kasar Sin Zou Xiaoming sun halarci bikin.
Gwamnatin kasar Sin da hukumar WFP sun yi hadin kai domin bayar da tallafin abincin da Sin ta bayar a wannan karo, ciki hadda sukari ton 500, wake ton 192, shimkafa ton 927.75 da man ja. Ya zuwa yanzu, wadannan kayayyaki sun isa Saliyo, kuma an rarraba yawancinsu.
A gun bikin, ministan harkokin wajen kasar Saliyo ya nuna cewa, tun bayan barkewar cutar Ebola a Saliyo, gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun baiwa kasar tallafi sosai. Tallafin abincin da Sin ta bayar a wannan karo na da ma'ana sosai wajen yaki da cutar Ebola, game da hakan, ya nuna godiya sosai ga taimako da gwamnatin kasar Sin ta bayar. (Amina)