in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya amince da ci gaba da taimaka wa Liberia wajen yaki da Ebola
2014-12-20 17:12:13 cri
Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya alkawarta ci gaba da baiwa kasar Liberia taimako a yakin da kasar ke yi da cutar Ebola.

Mr. Ban wanda ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labaru da ya gabatar a kasar ta Laberiya da hadin gwiwar shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf. Ya ce har kullum, MDD na hada karfi da karfe da mahukuntan Liberiya wajen dakile yaduwar cutar Ebola a kasar, kaza lika MDD za ta ci gaba da marawa Laberiya baya, ya zuwa lokacin da za a kai ga shawo kan yaduwar wannan cuta, tare da taimakawa wajen sake ginin kasar.

Ban Ki-moon ya kara da cewa, gamayyar kasa da kasa na farin ciki kwarai, game da sakamakon da aka samu a fannin rigakafi da na dakile yaduwar cutar ta Ebola, a sa'i daya kuma, ya jaddada cewa, ya kamata gamayyar kasashen duniya su ci gaba da karfafa matakan kawo karshen cutar, da kara hada gwiwa wajen dakile sake yaduwarta.

Bugu da kari, Ban Ki-moon ya ce, ya zama wajibi kasar Liberian ta fara shirin ginin kasa, bayan an kai ga kawo karshen cutar Ebola.

Daga nan sai ya yi alkawarin cewa, MDD za ta taimakawa kasar a wannan bangare, sa'an nan ya yi kira ga gamayyar kasashen duniya da su taimakawa Liberia a yunkurin tana farfado da yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin sauri. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China