Mahukunta a Saliyo sun kafa dokar hana fita ta kwanaki 5, a yankunan arewacin kasar, inda cutar Ebola ta fi shafa, a kokarin da ake yi na dakile bazuwar cutar.
Wani minista daga yankin arewacin kasar Alieu Kamara, ya ce, an dauki matakin rufe shaguna, da kasuwanni, da kuma dakatar da zirga-zirgar ababen hawa, domin cimma nasarar da aka sanya gaba. Haka kuma Kamara ya ce, an haramta tarukan addini, in banda bikin kirsimeti na ranar 25 ga wata ga mabiya addinin Kirista.
Wannan mataki dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun karuwar masu harbuwa da Ebola a arewaci da kuma yammacin kasar ta Saliyo, yankunan da kididdiga ke nuna na kunshe da kaso 2 bisa 3 na masu dauke da cutar a kasar. (Saminu)