in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta tura masana zuwa Senegal domin horas da jami'ai yaki da cutar Ebola
2014-12-27 17:27:56 cri
Jakadan Sin a kasar Senegal Xia Huang, da ministar kiwon lafiya ta kasar Senegal Eva Marie Coll Seck, sun rattaba hannu kan takardar amincewa da shirin tura masana kiwon lafiya biyu daga Sin zuwa Senegal, domin horas da jami'an lafiya hanyoyin dakile yaduwar cutar Ebola.

Hakan dai wani mataki ne na ci gaban kokarin da ake yi game da ilmantar da jami'an jiyya, da ma'aikatan kiwon lafiya, dabarun kare cututtuka masu yaduwa.

Bisa alkaluman da hukumar lafiya ta WHO ta fitar, kawo yanzu mutane sama da dubu 7 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola, wanda ta yadu a wasu kasashen yammacin nahiyar Afirka.

An ce wani wanda ya kamu da cutar ta Ebola ya shiga Senegal daga ketare, ko da yake an ce yanzu haka wannan mutum ya warke sarai. Kuma ya zuwa yanzu, ba a sake samun wani da ya kamu da cutar ta Ebola a Senegal ba.

A watan Nuwambar da ya gabata, gwamnatin Sin ta ba da kayayyakin agaji, da darajarsu ta kai kudin Sin RMB miliyan 5 ga Senegal, ciki hadda tufafin kariya, da na'urorin fesa magunguna da dai sauransu.

Ya yin bikin sa hannu kan wannan shiri, Seck ta bayyana cewa, tura kwararrun na Sin zuwa Senegal, ya sake bayyana dangantakar kut da kut dake tsakanin kasashen biyu. Ta ce Sin tana da fasahohi da dama na tinkarar barkewar cututtuka masu yaduwa. Fasahohin da zasu tallafawa Senegal kaiwa ga shawo kan cutar Ebola yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China