in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojin kiyaye zaman lafiya a Liberia ya warke bayan ya kamu da Ebola
2014-12-24 10:47:21 cri

A halin da ake ciki, wani sojin kiyaye zaman lafiya na MDD dake aiki a karkashin rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta MDD dake Liberia ya warke sarai bayan ya kamu da cutar Ebola.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya ce, sojin wanda asalin shi 'dan Nigeria ne a yanzu zai koma bakin aiki, kuma za'a ci gaba da duba lafiyar shi, tare da ba shi shawarwari da sa ido a kan al'amurran shi.

Dujarric ya ce, tun farko, wani gwaji da aka yi a Liberia ya nuna cewar, sojan ya harbu da cutar Ebola, hakan ya sa an dauke shi zuwa Netherlands a ranar 6 ga watan Disamba, kuma bayan ya warke sarai daga cutar sai aka mai da shi Liberia.

Liberia na daga cikin jerin kasashen da cutar Ebola ta fi yin kamari, daga nan sai Saliyo da Guinea.

Wani rahoto na nuni da cewar, wadanda suka mutu a sakamakon cutar sun fi yawa a Liberia a inda kididdiga ta nuna cewar, kawo ya zuwa yanzu mutane 3,290 ne suka rasa rayukansu a sakamakon cutar a Liberia.

Rahotan na MDD ya ce, a halin da ake ciki, wadanda ke harbuwa da cutar a Liberia suna ci gaba da raguwa, a kuma kasar Guinea, adadin na kan gaba kan baya, a kuma Saliyo, an daina samun sabbin wadanda ke kamuwa da cutar ta Ebola.

Hukumar lafiya ta MDD ta ce, kididdiga na nuna cewa, kawo ya zuwa yanzu wadanda suka kamu da cutar sun kai 18,603, kuma daga cikin wannan adadi, mutane 6915 sun rasa rayukansu. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China