Jami'in MDD mai kula da wannan cutar Ebola ya yi kashedi cewa, ya kamata mutane su yi takatsantsan yayin da suke zama tare da iyalansu a lokacin bukukuwan Kirsimati da sabuwar shekara.
Bayanai na nuna cewa, kasar Saliyo ce ta fi samun mutanen da suka kamu da cutar Ebola, inda aka tabbatar ko ake zaton mutane 9004 sun kamu da cutar Ebola a kasar, yayin da mutane 2582 daga cikinsu suka mutu.
Kana a kasar Liberia yawan mutanen da suka mutu a sakamakon cutar, ya kai 3384.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, yanzu haka an samu raguwar yaduwar cutar ta Ebola sakamakon daukar matakan rigakafi da yadda ake yaki da cutar yadda ya kamata.
Yadda ake binne gawawwakin mutanen da suka mutu a sakamakon cutar da killace mutanen da suka kamu da cutar su ne hanyoyi mafi kyau wajen hana yaduwar cutar. Burin tawagar musamman ta MDD kan yaki da cutar Ebola shi ne amfani da wadannan hanyoyin biyu a kowace kasa da ke fama da cutar daga ranar 1 ga watan Janairu na badi. (Zainab)