A yau ne ma'aikatar kiwon lafiya da tsara shirin haihuwa ta kasar Sin ta ba da labari kan shafinta na intanet da cewa, kasar Sin ta fara gwada ingancin allurar rigakafin cutar Ebola ta farko a kan mutane.
An labarta cewa, wannan allura ita ce ta uku a duk fadin duniya, wadda aka fara gwada ta a kan mutane, bayan kasashen Amurka da Canada. Hukumomin da abin ya shafa sun ce, wannan wani babban ci-gaba ne da kasar Sin ta samu wajen yaki da sabbin cututtuka masu yaduwa.(Tasallah)